BUKIN BUDE KAMFANIN MAI DAJI GLOBAL SERVICES DAKE NAN GARIN BIRNIN KEBBI.

Maigirma Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi Alh Babale Umar (Fagachin Yauri) ya wakilci  Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi wurin bude babban Kamfanin  Na'urorin more rayuwa na Alh Samaila Mabo Mai suna MAI DAJI GLOBAL SERVICES

Wanda Babban mataimaki na musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi ya samu halarta Alh Faruku Musa Yaro Enabo kuma amini ga MD na wannan katafaren Kamfani.

Maigirma PA Wanda yayi jawabi na maraba ga dukkan al-ummar da suka halarci bude wannan wurin, haka kuma Mukaddashin Gwamnan Jihar Kebbi, Fagachin Yauri yayi fatar alkhairi tareda Kara Kira ga al-ummar Jihar nan da sukara tashi tsaye wurin kir-Kira masana'antu ire iren wannan tareda shedamusu cewa kullum Gwamnatin Maigirma Gwamna Atiku Bagudu shirye take ta tallafawa jama'ar Jihar nan ta kowane bangare musamman ta bangaren kasuwanci.

Daga karshe Alh Faruku Musa Yaro  Enabo yayi addu'ar Allah sa albarka tareda rokon Allah yakara kawo ire iren wannan a Jihar Kebbi baki daya.

Yahaya Danjada
12/02/2020

Comments

Popular posts from this blog

Kebbi Guber: Kebbi Tribunal Admits Original Certificates Of Deputy Governor.

KBSG DISTRIBUTES N200M LIVELIHOOD GRANTS TO 2,000 BENEFICIARIES

KEBBI STATE GOVERNMENT CONDOLES WITH THE FAMILY OF LATE JOURNALIST.