BUKIN GARGAJIYA DA AL'ADUN RIGATTA NA KASAR ZURU
RAHOTANNIYadda Bikin RIGATA 2020 Ya Gudana A KebbiPublished 30 mins ago on February 23, 2020By Umar Faruk A jiya ne bikin Rigata na masarautar Yauri da ke daya daga cikin masarautun gargaji a jihar ta Kebbi. Masarautar Yauri tana da shekaru dari 500 da kafawa da kuma sarakuna 42 tun daga kafa masarautar zuwa yau da aka gudanar da Rigata a jiya a garin Yauri. Wanda an kwashe shekaru 45 ba’a gudanar wasar al’adun gargaji na Rigata , amma a shekara ta 2019 aka farfado da cigaba da bikin na al’adun gargaji na yawurawa, sai kuma a jiya 22 ga watan biyu na shekara ta 2020 da aka gudanar da bikin a garin na Yauri inda masarautar ta ciki babu maso katsin-tsinya a garin na Yauri kan gudanar da bikin na Rigata da kuma shedar irin yadda al’adun gargaji na yawurawa ke kayatarwa . Bikin dai ya samu halartar manyan mutane daga jihohin kasar nan kama tun daga jihohi yarbawa, igbo da kuma sauran sasan kasar kai harma da na wasu kasashen ketare kamar jamhuriyar Nijar da ta Benin da kuma sauransu. Sauran mahalarta taron bikin sun hada da kungiyoyin gwamnatin da kuma sarakuna gargaji na jihar ta Kebbi da na sauran wasu jihohin kasar nan . Haka kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu kamar kungiyar khaimiyyah da sauransu. A jawabinsa a matsayinsa na babban bako a wurin bikin Rigata a masarautar Yauri, Kakakin majalisar dokoki na kasa Femi Gbajamila ya ce ” kasar Nijeriya Allah ya albarkace ta da al’adun gargaji irin daban daban, saboda hakan yana kira ga al’ummar kasar Nijeriya cewa su cigaba da bada muhimmanci ga al’adun yankunan su don ta hanyar gudanar da bukukuwan al’adun gargaji a kasar zai taimakawa gwamnatotin jihohin kasar da ma gwamnatin tarayya wurin farfado da tattalin arzikin kasa ta habaka kudaden shiga a jihohi da kasa baki daya. Haka kuma ya kara da cewa bikin al’adun gargaji zai kara dankon zumunci a tsakanin al’ummar kasar Nijeriya da ma sauran wasu Mutane na kasashen waje. Bugu da kari ya ce” a majalisar dokoki ta kasa za su tabbatar da cewa sun bada muhimmanci da kuma goyon baya ga harakokin al’adun gargaji na mutanen kasar Nijeriya “. Har ilayau yace ” naga hanyar kara habaka tattalin arzikin kasa a cikin mintoti a bikin Rigata a garin Yauri da ke a jihar Kebbi”, Inji shugaban majalisar dokoki na tarayya Femi Gbajabiamila. Daga nan ya taya masarautar Yauri da kuma gwamnatin jihar Kebbi murnar gudanar da bikin Rigata a garin Yauri a jihar Kebbi, wanda yayin kira ga al’ummar masarautar Yauri da sauransu masarautun kasar Nijeriya da su cigaba da habaka al’adun su don ta hakan ne arzikinsu zai kara bunkasa ta hanyar yin hadin gwiwa da gwamnatotin jihohin da kuma gwamnatin tarayya kai har da hukumomin da ke saka jari kan habaka al’adun gargaji na kasar Nijeriya dana kasashen waje. Shima a nashi jawabin, ministan watsa labaru na kasa, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana goyon bayan ma’aikatarsa da kuma gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban Muhammadu Buhari wurin ganin cewar ta bada nata gudunmuwa da kuma goyon baya wurin tabbatar da cewar an habaka tattalin arzikin kasa ta hanyar bunkasa al’adun gargaji na mutanen kasar Nijeriya wanda bikin Rigata daya daga cikin wanda gwamnatin tarayya zai ta mayar da hankali don kara tabbatar da cewar ta hanyar habaka al’adun gargaji ya kasar samar da ayyukkan yi ga matasan kasar nan . Haka kuma ministan ya kara da cewar” irin bayyanan da ke fito wa kan bikin Rigata a Yauri da ke jihar Kebbi kan irin arzikin kasuwanci da ake gudanar wa daga bakin ruwan kogo na Yauri da ake gudanar bikin Rigata dukkan shekara-shekara wanda ake daukar kayan amfanin gona da jirgin kwalekwale zuwa kasashen Afirka ta Yamma kamar Ghana, Mali, jamhuriyar Nijar da kuma Benin da kuma sauran ya zama gaskiya bisa ga abinda na ganan ma ido na a wurin bikin Rigata a garin Yauri da ke a jihar Kebbi”. Saboda hakan a matakin gwamnatin tarayya zai mu tabbatar da cewar ” ire-iren wadannan bukukuwan al’adun gargaji sun samu karbuwa a kasashen duniya Insha Allah. Hakazalika Sarkin na Yauri ya gabatar da nashi jawabi, Alhaji Zayyanu Abdullahi ya godewa Allah kan samun nasarar gudanar da bikin Rigata cikin nasara batare da wata matsala ba . Yece” duk wanda ya samu halartar bikin Rigata zai tabbatar da cewar masarautar Yauri wuri ne da ke da hanyoyin samar da ayyukkan yi ga al’ummar kasar nan ta hanyar al’adun gargaji na masarautar ta Yauri da kuma sana’ar kamun kifi da kuma sayar da shi ga wasu ‘yan kasuwar jihohin kasar Nijeriya da kuma fitar dashi zuwa kasuwannin kasashen Afirka ta Yamma. Saboda hakan yana kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnatotin jihohin da kuma na tarayya da su shigo cikin wannan al’adun gargaji na mutanen masarautar Yauri don kara habaka tattalin arzikin kasar Nijeriya da kuma yin amfani da wannan don kara samar da ayyukkan yi ga jama’ar kasar nan. Daga karshe ya godewa dukkan manyan gwamnatin tarayya da kuma na jihar Kebbi da sauran jihohin kasar kan karba kiran goron gyata don gudanar bikin Rigata cikin nasara . Amadadin mutanen masarautar Yauri da kuma ni kaina ” Muna godiya sosai”. Da yake jawabinsa tun farko, Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana jindadinsa kan irin nasarar da aka samu na gudanar da bikin Rigata cikin kwanciyar hankali da kuma irin manyan bakin da samu halartar bikin. Ya cigaba da bayyana cewar” jihar Kebbi Allah ya albarka ceta da arzikin ma’adanan kasa da kuma al’adun gargaji na mutanen masarautun jihar daya daga cikin su shine bikin Rigata da a gudanar a garin Yauri da ke a jihar ta Kebbi a karkashin jagorancina zamu tabbatar da cewar ” mun farfado da tattalin arzikin al’adun gargaji na masarautun jihar Kebbi”, haka kuma zamu yi iya kokarinmu na ganin cewar gwamnatin tarayya da hukumomin da ke saka jari kan al’adun gargaji sun kawo dauke da gudunmuwa kan shirya bukukuwan al’adun gargaji da kuma saka jari don kara samar da ayyukkan yi ga jama’ar kasar Nijeriya dana jihar ta Kebbi . Bisa irin kokarin gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban Muhammadu Buhari yasa ayau da ake gudanar da bikin Rigata a garin Yauri haka kuma za’a kaddamar da bikin hako ma’adanai duk a cikin masarautar ta Yauri. Ya kara da cewar “Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin ma’aikatar kula da ma’adanai da karafa tare da sauran mambobbin tawagar da gwamnatin tarayya ta turo a jihar ta Kebbi don gudanar da aikin tantance kamfanin da zasu hako ma’adanai a yankunan na masarautar Yauri da kewaye don inganta hanyoyin samar da kudaden shiga na jihar Kebbi da kuma gwamnatin tarayya . Haka kuma ya godewa wakilan jama’ar jihar Kebbi da ke a majalisar dokoki kan irin namijin kokarin da suke yi kan ganin cewar wannan bikin al’adun gargaji na Rigata ya samu nasarar gudanar wa . Daga karshe ya godewa Sarkin na Yauri da kuma al’ummar masarautar kan irin gudunmuwar da suka bayar don tabbatar da cewar bikin samu nasarar gudanar .
Comments
Post a Comment