AL-UMMAR GARIN RINAYE DAKE GARIN GWANDU SUN ZIYARCI KWAMISHINAN KANA NAN HUKUMOMI DA MASARAUTU NA JIHAR KEBBI

AL-UMMAR GARIN RINAYE DAKE GARIN GWANDU SUN ZIYARCI KWAMISHINAN KANA NAN HUKUMOMI DA MASARAUTU NA JIHAR KEBBI* 


Maigirma Kwamishinan Kananan hukumomi da masarautu na Jihar kebbi Rt. Hon. Hassan Shallah  ya karbi bakuncin al-ummar garin Rinaye dake Mazabar Malisa a Karamar hukumar mulki ta Gwandu.

Wannan tawagar ta samu jagorancin hakimin Rinaye da wasu daga cikin shuwagabannin wannan yankin.

Tawagar sun zo ne da korafin rashin wutar lantarki a wannan yankin na Garin Rinaye dake Malisa, inda nan take Rt. Hon. Hassan Shallah ya nemi Kwamishinan Wuta da Ruwa na Jihar kebbi Hon. Nura Kangiwa (DU) domin gabatar da wannan koken.

Kwamishinan na Ruwa da wuta da yake jawabi ya Basu tabbacin Samar da wutar lantarki a wannan yankin tareda tabbatar musu da cewa Gwamnatin Maigirma Sanata Abubakar Atiku Bagudu a shirya take ko yaushe ta saurari irin wannan koken ta kuma Samarda dukkan bukatu domin Samarda ingantattar rayuwa ga al-ummar jihar kebbi.

Haka zalika Hakimin garin Rinaye yayi godiya ga Kwamishinan Wuta da Ruwa na Jihar kebbi bisaga cika alqawarin Samar da isassun ruwan sha da yayi musu a wannan garin na Rinaye.

Comments

Popular posts from this blog

ƘUNGIYAR 'YAN SAKAI MAI SUNA (AMANA FARMERS) A YAU TA KAWO TALLAFI GA GWANNATIN JAHAR KEBBI NA ABINCI DA TAKIN ZAMANI KAN ƁARNAR RUWA.

MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KEBBI SANATA UMAR TAFIDA YA KARBI BAKUNCIN SHUWAGABANNIN KUNGIYAR KANSILOLI TA JIHAR KEBBI