BUKIN YAYE DALIBBAI 21 NA MADRASATUL UMAR IBNUL KHADDAB LITAHFIZUL QUR'AN WADDARASATIL ISLAMIYYA GWADANGAJI, BIRNIN KEBBI, JAHAR KEBBI

BUKIN YAYE DALIBBAI 21 NA MADRASATUL UMAR IBNUL KHADDAB LITAHFIZUL QUR'AN WADDARASATIL ISLAMIYYA GWADANGAJI, BIRNIN KEBBI, JAHAR KEBBI.

A yau Assabar 17-10-2020 aka gudanar da bukin yaye Dalibbai 21 na Makarantar Umar Dan Khaɗɗab dake Gwadangaji, anan cikin garin Birnin Kebbi.

Bukin yasami halartar Mai girma Khadimuddeen Alh Faruku Musa Yaro (Enabo) da 'yan tawagarshi da suka haɗa da:

Alh Yusuf Musa Yaro
Alh Ismail Mabo 
Alh Misbahu Aliyu
Alh Haruna Ladan
Alh Aminu Kura 
Alh Usman Osho
Alh Atiku Yaro

Dayake jawabi, Mai girma Khadimudden, ya jawo hankalin iyaye kan halartar irin wannan taron na addini saboda muhimmancinshi a wajen Mahalicci. Ya ƙara da cewa shirye yake a duk lokacin hidimar addini ta tashi. Haka kuma ya bada tashi gudunmuwar kamar haka:

Alh Faruku Musa Yaro -- Kyautar Naira Dubu Ashirin (#20,000) ga kowanne Dalibi su 21

Kyautar Umrah ga waɗanda zasu ci gasar dake tafe shekara mai zuwa.

Kyautar Naira #10,000 ga wata Daliba macce wacce tayi nasiha.

Kyautar Naira Dubu biyar biyar ga waɗanda sukayi Musabaƙa

Maza #5,000
Mata #5,000

Hajiya Koli           --  zata gina rijiyar Ruwa da tankin ruwa

Alh Ismail Mabo -- Bulo na gina dubu biyu (2,000) da Jakar Siminti ƙwara (20)

Alh Aminu Kura -- Bulo dubu ɗaya (1,000)

Alh Misbahu Aliyu -- shine yasayi Fili kuma ya aza tubalin ginin Makarantar.

Alh Usman Osho -- Motar Yashi (20)

Dayake maida jawabi Shugaban Makarantar yayi godiya ga wannan aikin alkhairi da akayi ga addinin ALLAH, ya kuma roƙi ALLAH daya sakawa waɗannan bayin nashi da mafificin alkhairi.

Gwadangaji, Birnin Kebbi.
17-10-2020

Comments

Popular posts from this blog

Kebbi Guber: Kebbi Tribunal Admits Original Certificates Of Deputy Governor.

KBSG DISTRIBUTES N200M LIVELIHOOD GRANTS TO 2,000 BENEFICIARIES

KEBBI STATE GOVERNMENT CONDOLES WITH THE FAMILY OF LATE JOURNALIST.