ƘUNGIYAR 'YAN SAKAI MAI SUNA (AMANA FARMERS) A YAU TA KAWO TALLAFI GA GWANNATIN JAHAR KEBBI NA ABINCI DA TAKIN ZAMANI KAN ƁARNAR RUWA.
ƘUNGIYAR 'YAN SAKAI MAI SUNA (AMANA FARMERS) A YAU TA KAWO TALLAFI GA GWANNATIN JAHAR KEBBI NA ABINCI DA TAKIN ZAMANI KAN ƁARNAR RUWA.
A yau Assabar 26-09-2020, Ƙungiyar Amana Farmers da ake kira da (AFGASAN) a turance sun bada gudunmuwa ga Gwannatin Jahar Kebbi na Irin Shinkafa, Masara, Gero da Takin Zamani a fadar Gwannatin Jahar Kebbi dake nan Birnin Kebbi.
Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Alh Ahmad Danbeguwa shine ya jagoranci bada wannan tallafin amadadin Ƙungiyar. Dayake jawabi, ya bayyana cewa sunzo Jahar ne domin jajantawa ga al'ummar Jahar kan ibtila'in da aka samu na ɓarnar ruwa, ya ƙara da cewa Jahar Kebbi da Mai Girma Gwamnan Kebbi uwaye ne garesu saboda irin rawar da Gwamnan ke takawa domin farfaɗo da noma da kuma ci da Najeriya gaba ɗaya.
Daga cikin gudunmuwar da suka basuwa ga Gwannatin Kebbi, akwai:
Irin Shinkafa 2019
Takin Zamani 600
Masara 560
Gero 535
Dayake Jawabin godiya, Mai Girma Gwamnan Kebbi, Shugaban Gwannonin Najeriya na Jamɓiyar APC, Sarkin Noman Najeriya, Sen. Abubakar Atiku Bagudu yace Gwannatinsa tana godiya da ƙoƙarin da wannan Ƙungiyar tayi ga al'ummarshi kana yace ƙofa a buɗe take ga duk wanda zai iya bada tashi gudunmuwa domin tunƙarar Noman rani.
Daga ƙarshe Mai girma Gwamnan yayi musu albishir da cewa Gwannatinsa shirye take ta taimakawa manya da ƙananan Manoma nan bada jimawa ba, ya kuma yi musu fatan alheri a duk inda suka samu kansu.
Daga cikin waɗanda suka halarci wannan taron Mai albarka, akwai :
Hadimi na Musamman (P A) ga Mai Girma Gwamnan Kebbi
Alh Faruku Musa Yaro (Enabo)
Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Masarautu
Hon Hassan Shallah Gwandu
Shugaban Ƙungiyar na Jaha
Alh Atiku Chiroma da Exco ɗinshi a matakin Jaha
Shugabannin Ƙungiyar na Ƙasa da dai sauran Jama'a.
Daga Fadar Gwannatin Jahar Kebbi,
Birnin Kebbi.
26-09-2020
Comments
Post a Comment