NOMA TUSHEN ARZIKI

NOMA TUSHEN ARZIKI.

Maigirma Gwamnan Jahar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu MATAWALLEN GWANDU yabada umurnin hannata Tarikitoti Sabbi Guda Goma Sha Biyar 15 a Kananan Hukumomi Ukku 3 dake Yankin Kasar Zuru A Jahar Kebbi domin yima Talakkawan Yankin da Fitinar Barayin Shanu tahanama Samun noman Shanu don noma a Damanar bana.

Kananan Hukumomin sun Hada da

1. Zuru Tarikitoti Guda 3
2. Danko Wasagu Guda 7
3. Sakaba Guda 5

Tuni Kwamishinan Ma'aikatar Gona da Albarkatun Kasa na Jahar Kebbi Alh Maigari Abdullahi Dakingari ya hannata su ga Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautun Jahar Kebbi Rt. Hon Hassan Shallah Gwandu inda shi kuma ya hannata su ga Shugabannin Kananan Hukumomin su Ukku Karkashin Jagorancin Hon Kabiru Muhammad Rafi na Karamar Hukumar Mulki ta Zuru.

Da yake Jawabi Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautun Jahar Kebbi Rt. Hon Hassan Muhammad Shallah Gwandu ya jawo Hankalin Shugabannin Kananan Hukumomin da cewa suyi Kokari suyi aiki da Tarikitotin kamar yadda Maigirma Gwamna ya bukata ayi a iya Yankin Kananan Hukumomin su batareda an ketara wata jaha ba Kuma ayi aikin Kyauta ga Talakkawa.

Haka Shima Kwamishinan Ma'aikatar Gona Yaqara dacewa kasancewar Maigirma Gwamna yabaiwa Sha'anin Noma muhimmanci shi yassa yabada umurnin bada wadannan Kayan aikin bada wasaba.

Da yake Godiya amadadin Shugabannin Kananan Hukumomin Danko Wasagu da Sakaba Hon Kabiru Rafi Zuru yayi Godiya ga Allah Subhanahu Wata'ala bisa wannan Ni'ima da yayi musu na samun wadannan Kayan aiki inda yaqara Godiya ga Maigirma Gwamna Sanata Bagudu tareda Tabbatar dacewa in Shaa Allahu zasuyi amfani dasu kamar yadda aka umurce su.

Daga Karshe an hannanta Tarikitotin a Gaban Sakatarori Guda biyu Sakataren Mai'aikar Gona Mr Joe Aiki da Na Kananan Hukumomi Alh Sani Yeldu, Yan Jarida da sauran Ma'aikatan KARDA.

Rahoton
Yahuza Zaki Gwandu
Daga Karda Birnin Kebbi
Jahar Kebbi, Nijeriya.
Larba 30/06/2021.

Comments

Popular posts from this blog

Kebbi Guber: Kebbi Tribunal Admits Original Certificates Of Deputy Governor.

KBSG DISTRIBUTES N200M LIVELIHOOD GRANTS TO 2,000 BENEFICIARIES

KEBBI STATE GOVERNMENT CONDOLES WITH THE FAMILY OF LATE JOURNALIST.