AL-UMMAR GARIN RINAYE DAKE GARIN GWANDU SUN ZIYARCI KWAMISHINAN KANA NAN HUKUMOMI DA MASARAUTU NA JIHAR KEBBI* Maigirma Kwamishinan Kananan hukumomi da masarautu na Jihar kebbi Rt. Hon. Hassan Shallah ya karbi bakuncin al-ummar garin Rinaye dake Mazabar Malisa a Karamar hukumar mulki ta Gwandu. Wannan tawagar ta samu jagorancin hakimin Rinaye da wasu daga cikin shuwagabannin wannan yankin. Tawagar sun zo ne da korafin rashin wutar lantarki a wannan yankin na Garin Rinaye dake Malisa, inda nan take Rt. Hon. Hassan Shallah ya nemi Kwamishinan Wuta da Ruwa na Jihar kebbi Hon. Nura Kangiwa (DU) domin gabatar da wannan koken. Kwamishinan na Ruwa da wuta da yake jawabi ya Basu tabbacin Samar da wutar lantarki a wannan yankin tareda tabbatar musu da cewa Gwamnatin Maigirma Sanata Abubakar Atiku Bagudu a shirya take ko yaushe ta saurari irin wannan koken ta kuma Samarda dukkan bukatu domin Samarda ingantattar rayuwa ga al-ummar jihar kebbi. Haka zalika Hakimin garin Rina...
ƘUNGIYAR 'YAN SAKAI MAI SUNA (AMANA FARMERS) A YAU TA KAWO TALLAFI GA GWANNATIN JAHAR KEBBI NA ABINCI DA TAKIN ZAMANI KAN ƁARNAR RUWA. A yau Assabar 26-09-2020, Ƙungiyar Amana Farmers da ake kira da (AFGASAN) a turance sun bada gudunmuwa ga Gwannatin Jahar Kebbi na Irin Shinkafa, Masara, Gero da Takin Zamani a fadar Gwannatin Jahar Kebbi dake nan Birnin Kebbi. Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Alh Ahmad Danbeguwa shine ya jagoranci bada wannan tallafin amadadin Ƙungiyar. Dayake jawabi, ya bayyana cewa sunzo Jahar ne domin jajantawa ga al'ummar Jahar kan ibtila'in da aka samu na ɓarnar ruwa, ya ƙara da cewa Jahar Kebbi da Mai Girma Gwamnan Kebbi uwaye ne garesu saboda irin rawar da Gwamnan ke takawa domin farfaɗo da noma da kuma ci da Najeriya gaba ɗaya. Daga cikin gudunmuwar da suka basuwa ga Gwannatin Kebbi, akwai: Irin Shinkafa 2019 Takin Zamani 600 Masara 560 Gero ...
MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KEBBI SANATA UMAR TAFIDA YA KARBI BAKUNCIN SHUWAGABANNIN KUNGIYAR KANSILOLI TA JIHAR KEBBI Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi OFR, ya karbi bakuncin Shugabancin Kungiyar Kansiloli na jihar kebbi. Da yake jawabi shugaban kungiyar ta kansilolin na jihar kebbi, yace sun kawo wannan ziyarar ne domin taya murnar kama aiki da Kuma sada zumunci, kansilan ya kara da cewa kungiyar su ta shirya tsaf domin bayar da hadin kai don nasarar Gwamnatin Comrade Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu da Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi. Mataimakin Gwamnan ya nuna jindadin shi tare da yin godiya matuka bisa ga irin mutuntawar da kungiyar tayi mishi ya Kuma basu tabbacin goyon bayan shi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Hon. Yahaya Danjada Arg. SSA ON NEW MEDIA 5/06/2023
Comments
Post a Comment