SHEKARU BIYU DA APC TA YI TANA MULKI, ILIMI YA SAMI KOMA-BAYA A JIHAR KEBBI
SHEKARU BIYU DA APC TA YI TANA MULKI, ILIMI YA SAMI KOMA-BAYA A JIHAR KEBBI
Daga Atiku Sani Birnin Kebbi
Masana harkokin Ilimi sun tabbatar da cewa an sami koma-baya a bangaren Ilimi tun daga lokacin da APC ta kama gwamnati a jihar Kebbi .Masu tsokacin sun tabbatar da haka ne ta la'akari da yadda Malaman makarantu ke shan wuya dangane da albashi da kuma yadda aka daina samar da kayan aiki a makaruntu fun bayan faduwar gwamnatin PDP. Inda suka tabbatar da cewa biyan albashi ga malamai da kuma Samar da kayan aiki su ne kashin bayan samun ilmi mai nagarta ga kowace al'umma.
Wani abin da kuma ya kara durkusar da harkar ilmi a jihar ta Kebbi shi ne,yadda gwamnatin ta APC ta dakatar da biyan kudin jarabawar kammala sakandare ga daliban jihar, kamar yadda gwamnatin da ta gabata ta PDP ta yi.Wanda hakan ya jawo da yawa daga daliban rashin samun damar rubuta jarabawar,saboda iyayensu ba su da zarafin biya masu kudin jarabawoyin,kuma da yawa suka koma barayi ko yan zauna-gari-banza.
Masanan sun kara da cewa,a lokacin gwamnatin PDP tana daukar nauyin dalibai yan asalin jihar Kebbi domin karo karatu a kasashen waje, gwamnatin APC ta tsai da wannan,kuma hakan ba karamin koma-baya ba ne ga harkar Ilimi.
Bugu da kari,gwamnatin PDP takan dauki sabbin malamai daga lokacin zuwa lokacin don cike gurabun da ake da su,amma wannan gwamnatin tunda ta hau ba ta dauki Malam ko daya ba,wanda kuma har alkawari ta yi na daukar malaman amma har yau ta kasa cikawa.
Wadannan su ne wasu daga cikin dalilan da masanan suka ba da wadanda suka tabbatar da cewa gwamnatin APC ta gaza a jihar Kebbi ta bangaren Ilimi, duk da kurin da take yi na cewa za ta gyara bangaren Ilimi a jihar ta kebbi.
DON HAKA A BA MU A HUTA.
Kodineta SYB Bk
Comments
Post a Comment