BUKIN YAYE DALIBBAI 21 NA MADRASATUL UMAR IBNUL KHADDAB LITAHFIZUL QUR'AN WADDARASATIL ISLAMIYYA GWADANGAJI, BIRNIN KEBBI, JAHAR KEBBI . A yau Assabar 17-10-2020 aka gudanar da bukin yaye Dalibbai 21 na Makarantar Umar Dan Khaɗɗab dake Gwadangaji, anan cikin garin Birnin Kebbi. Bukin yasami halartar Mai girma Khadimuddeen Alh Faruku Musa Yaro (Enabo) da 'yan tawagarshi da suka haɗa da: Alh Yusuf Musa Yaro Alh Ismail Mabo Alh Misbahu Aliyu Alh Haruna Ladan Alh Aminu Kura Alh Usman Osho Alh Atiku Yaro Dayake jawabi, Mai girma Khadimudden, ya jawo hankalin iyaye kan halartar irin wannan taron na addini saboda muhimmancinshi a wajen Mahalicci. Ya ƙara da cewa shirye yake a duk lokacin hidimar addini ta tashi. Haka kuma ya bada tashi gudunmuwar kamar haka: Alh Faruku Musa Yaro -- Kyautar Naira Dubu Ashirin (#20,000) ga kowanne Dalibi su 21 Kyautar Umrah ga waɗanda zasu ci gasar dake tafe shekara mai zuwa. Kyautar Naira #10,000 ga wata Daliba macce wacce tayi nasiha. K...