ƘUNGIYAR 'YAN SAKAI MAI SUNA (AMANA FARMERS) A YAU TA KAWO TALLAFI GA GWANNATIN JAHAR KEBBI NA ABINCI DA TAKIN ZAMANI KAN ƁARNAR RUWA.
ƘUNGIYAR 'YAN SAKAI MAI SUNA (AMANA FARMERS) A YAU TA KAWO TALLAFI GA GWANNATIN JAHAR KEBBI NA ABINCI DA TAKIN ZAMANI KAN ƁARNAR RUWA. A yau Assabar 26-09-2020, Ƙungiyar Amana Farmers da ake kira da (AFGASAN) a turance sun bada gudunmuwa ga Gwannatin Jahar Kebbi na Irin Shinkafa, Masara, Gero da Takin Zamani a fadar Gwannatin Jahar Kebbi dake nan Birnin Kebbi. Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Alh Ahmad Danbeguwa shine ya jagoranci bada wannan tallafin amadadin Ƙungiyar. Dayake jawabi, ya bayyana cewa sunzo Jahar ne domin jajantawa ga al'ummar Jahar kan ibtila'in da aka samu na ɓarnar ruwa, ya ƙara da cewa Jahar Kebbi da Mai Girma Gwamnan Kebbi uwaye ne garesu saboda irin rawar da Gwamnan ke takawa domin farfaɗo da noma da kuma ci da Najeriya gaba ɗaya. Daga cikin gudunmuwar da suka basuwa ga Gwannatin Kebbi, akwai: Irin Shinkafa 2019 Takin Zamani 600 Masara 560 Gero 535 Dayake Jawabin godiya, Mai Girma Gwamnan Kebbi, Shugaban