SHEKARU BIYU DA APC TA YI TANA MULKI, ILIMI YA SAMI KOMA-BAYA A JIHAR KEBBI
SHEKARU BIYU DA APC TA YI TANA MULKI, ILIMI YA SAMI KOMA-BAYA A JIHAR KEBBI Daga Atiku Sani Birnin Kebbi Masana harkokin Ilimi sun tabbatar da cewa an sami koma-baya a bangaren Ilimi tun daga lokacin da APC ta kama gwamnati a jihar Kebbi .Masu tsokacin sun tabbatar da haka ne ta la'akari da yadda Malaman makarantu ke shan wuya dangane da albashi da kuma yadda aka daina samar da kayan aiki a makaruntu fun bayan faduwar gwamnatin PDP. Inda suka tabbatar da cewa biyan albashi ga malamai da kuma Samar da kayan aiki su ne kashin bayan samun ilmi mai nagarta ga kowace al'umma. Wani abin da kuma ya kara durkusar da harkar ilmi a jihar ta Kebbi shi ne,yadda gwamnatin ta APC ta dakatar da biyan kudin jarabawar kammala sakandare ga daliban jihar, kamar yadda gwamnatin da ta gabata ta PDP ta yi.Wanda hakan ya jawo da yawa daga d...