SABON MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KEBBI, SANATA UMAR TAFIDA YA KARBI RANTSUWAR KAMA AIKI
Yau 29/05/2023 sabon Mataimakin Gwamnan Jihar kebbi, Sanata Umar Abubakar (Tafidan Kabi) OFR, ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar kebbi a babban fiin wasanni na tunawa da Sarki Haliru Abdu dake helikwatar jihar kebbi wato birnin kebbi. Mataimakin Gwamnan bayan karbar rantsuwar kama aiki nan take ya garzaya ofishin sa domin dubiya da Kuma shirin kama aiki kamar yadda doka ta tanada. Haka zalika sabon Mataimakin Gwamnan ya samu tarba ta musamman daga masoya dake kowane lungu a garin Argungu, inda kaitsaye yawuce fadar Mai Martaba Sarkin kabin Argungu domin neman tubarrakin shi, da yake nashi jawabi Mai Martaban ya Kara da karfafa al'ummar Jihar nan dasu bayar da dukkan goyon bayan da ya dace ga wadannan sabbin shuwagabannin bisaga irin ayukkan alheri da aka shede su dashi tun basu samu dama ba ya Kuma Kara da yimu su addu'o'i na musamman domin samun nasara a wannan Shugabancin da ya rataya akan su.