KIRAYE KIRAYEN DA AL-UMMAR KARAMAR HUKUMAR MULKI TA GWANDU GA KAIGAMAN GWANDU DOMIN YA FITO TAKARAR KUJERAR DAN MAJALISAR TARAYYA MAI WAƘILTAR GWANDU, ALIERO DA JEGA.
KIRAYE KIRAYEN DA AL-UMMAR KARAMAR HUKUMAR MULKI TA GWANDU GA KAIGAMAN GWANDU DOMIN YA FITO TAKARAR KUJERAR DAN MAJALISAR TARAYYA MAI WAƘILTAR GWANDU, ALIERO DA JEGA. Bayan kwashe tsawon lokaci ana kiraye kirayen Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar Kebbi Rt. Hassan Shallah (Kaigaman Gwandu) da ya fito takarar kujerar ɗan majalisar tarayya don ya waƙilci al-ummar Gwandu, Jega da Aliero bisaga chanchantar shi da kasan cewar shi gogaggen ɗan siyasa kuma ma'aikacin gwamnati. Shuwagabannin jam'iyyar APC, 'yan kasuwa, Malaman addini, Manyan ma'aikatan gwamnati, yan boko da sauran jama'ar garin Gwandu sunyi cincirindo a gidan Kwamishinan dake unguwar Shallah a garin Gwandu domin gabatar da Wannan buƙatar ga Maigirma Kwamishinan. Yau juma'a 6/05/2022 Maigirma Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar Kebbi Rt. Hon. Hassan Shallah ya saurari wannan ƙudurin na al-umma ya kuma tabbatar mu su da ami...