Jagaban Gwandu yabada gudunmuwar ₦1.m ga Makarantar Sheikh Abubakar Nassarawa.
Jagaban Gwandu yabada gudunmuwar ₦1.m ga Makarantar Sheikh Abubakar Nassarawa. A yau Lahadi 7-11-2021, Mai girma Hadimi na Musamman (P.A) ga Mai girma Gwamnan Jahar Kebbi Alh Faruku Musa Yaro Enabo (Jagaban Gwandu) ya halarci Walimar Saukar Alƙur'ani Mai Tsalki na Makarantar Marigayi Sheikh Abubakar Nassarawa wadda ake kira Madrasatul Abdullahi Bin Mas'ud ƙarƙashin Makarantar Sir Haruna Rasheed dake garin Birnin Kebbi, Jahar Kebbi. Mai girma Jagaban, yace a kullum burinshi shine tallafawa addinin Musulunci ta duk hanyar da yasamu dama, ya ƙara da cewa ilmi musamman na addini shine gishirin zaman lafiya da rayuwa ingantacciya, saboda haka yake ƙoƙari iya ƙoƙarinshi domin taimakon addini. Ya bayyana cewa amadadin shi kanshi da iyalanshi da abokkanshi da 'yan uwanshi ya bada kyautar Naira miliyan Ɗaya ga Makarantar, wanda yace: Naira Dubu Ɗari Biyar (#500,000) ga Dalibban da suka sauke Alkur'ani su (81) Naira Dubu Ɗari Biyar (#250,000) ga Malamman Makarantar. Haka zalika...